Hukumar Tara Kuɗaɗen Haraji ta kasa (FIRS) ta bayyana adadin kudaden da ta karɓa na haraji inda tace ya kai naira tiriliyan 5.5 tsakanin watan Janairu zuwa watan Yunin wannan shekarar.
Shugaban hukumar Muhammad Nami ne ya bayyana haka a lokacin taron Majalisar tattalin arziki ta ƙasa da ya gudana a jiya Alhamis a fadar gwamnati de ke Abuja.
Wannan ne karo na farko da hukumar ta tara adadi mafi yawa na kuɗin haraji a cikin wata shida, kamar yadda sanarwar hukumar ta bayyana.
Rahoton da Muhammad Nami ya gabatar wa majalisar tattalin arzikin, ya nuna cewa abin da hukumar ta tara ya zarta abinda ta ƙiyasta samu a cikin rabin shekarar.
Tun da farko hukumar ta ƙiyasta tara naira tiriliyan 5.3 a cikin wata shidan farko na shekarar.
Rahoton ya kuma nuna cewa kuɗin harajin da hukumar ta tara a ɓangaren man fetur, naira tiriliyan 2.03 ne ya fi yawa cikin harajin da hukumar ta tara.
Sai kuma naira tiriliyan 3.76 da hukumar ta tara daga sauran bangarori.