Daga Jamila Sulaiman Aliyu
Gwamnatin jihar Kano ta Sha alwashin taimakawa yan jaridu mata ta fuskar samun horo akan ayyukansa da kuma basu dama su taimakawa mata da kananan yara kwamishinan yada labarai na jihar Kano
Honarabil Baba Halilu Dantiye ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Yayin ziyarar da kungiyar mata yan’jaridu(nawoj) sukaka masa a offishinsa dake ma,aikatar yada labarai ta jiha.
kwamishinan yace zasu duba a irin tsare tsaren su a gwannatance su saka kungiyar ciki don suci gajiyar tsare tsaren musamman itin Shirin kungiyar na kula da masu yoyon fitsari da kuma yan gudun hijira da sauran marasa karfi dake fadin jihar nan.
shugabar kungiyar mata yan’jaridu (nawoj) Haj Hafsat sani Usman tace sun gamsu da irin tarbar da akayi musu musamman tafiya tare dasu da gwamnati ta alkawarta domin kungiyar hakan shine fatanta a ringa damawa da ita a ko wane bangare na gwamnati ta kuma Mika godiyar kungiyar ga kwamishinan tare da shan alwashin bawa mara da kunya
A nata jawabin sakatariyar kungiyar Elizabeth yila Lamido ta bayyana cewa idan suka samu dama zasu tallafawa mata marasa karfi tare da amsa Kiran kwamishinan bisa bukatar kirkirar shirye shiryen da zasu amfani mata da kananan yara.
Honarabil Dantiye ya ce gwamnati ta kirkiri Abubuwan tallafawa mata musamman ta furkar samat musu da abinci ta yadda zai Kai lungu da sako na fadin jihar nan dubo da irin halin da aka tsinci Kai a rayuwar yau da kullum