Kungiyar masu hada hadar magunguna ta kasa reshen jihar kano dake kasuwar malam kato a nan birnin kano,ta jaddada bayar da goyan bayanta ga Hukumomin dake da alhakin kawar da gurbatattun magunguna a jihar kano.
Shugaban Kungiyar Mohammed Musubahu yahaya ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai dangane da wani rahoto da wasu suka fitar a kafafen sadarwa akan ‘ya’yan Kungiyar.
Shugaban yace, Kungiyar masu hada hadar magani ba za ta zuba ido wasu daidaikun mutane da ba su da alaka da sana’ar siyar da magani su rika shafawa ‘ya’yanta kashin kaji.
Yace, Sakamakon gabaren da Kungiyar kasuwar magani ta jihar kano, ta dauka na ganin an kawo sauyi a bangaren sana’ar,Sai wasu mutane da suke bukatar Sai sun durkusar da kananan Yankasuwar da basu da karfin jari suka bijiro da Sai Alumma sun koma kasuwar Dangwauro wadda ta fi karfin da yawa daga cikin Yankasuwar.
Mohammed Musubahu,ya bayyana cewa,Wadanda suke da bukatar Sai Alumma sun tashi sun koma kasuwar Dangwauro,Sun hada kai ne da Wasu masu ruwa da tsaki akan kasuwar ta Dangwauro, inda suka zuba kudadensu a matsayin hannun jari domin Durkusar da Kananan masu karamin jari da Leburorin dake fafutukar Neman yadda za su ciyar da iyalansu da Yanuwansu.
A don haka Shugaban yace, Shugabancin Kungiyar ba zai gajiya ba wajen fitar da batagarin mutane daga cikin Yankasuwar magani domin Samar da kyakyawan yanayi da taimakawa yunkurin Gwamnati mai ci na kakkabe baragurbi dake safarar muggun kwayoyi da kasuwancin magunguna da Wa’adinsu ya kare domin Alummar jihar kano da ma kasa baki daya su samu magunguna da kare Lafiyar Alumma.
Shugaban Kungiyar kasuwar maganin ya kara da cewa, Kungiyar da ta zo a cikin kashi Dari na masu shigowa da gurbatattun magunguna, ta magance kashi Tamanin da biyar ta yin hadin gwiwa da Jami’an tsaro da suka hadar da Hukumar Hana sha da fataucin muggun kwayoyi da Jami’an yansanda da sauran Hukumomin dake da Hurumi akan dakile gurbatattun magunguna ta hanyar Samar da kwamati na musamman da yake yawo lungu da sako na kasuwar domin gano masu sana’ar ba bisa yadda Doka ta tanada ba.
Daga karshe Shugaban yayi kira da Gwamnati, da sauran Hukumomin dake da Alhaki akan wannan lamari da su kawowa Yankasuwar magani daukin gaggawa musamman, kananan Yankasuwar, bisa Zalinci da wasu masu hannu shuni suke son yiwa kananan Yankasuwar da Wadanda suke leburanci domin ciyar da iyalansu da kuma, Sharrin da suke kokarin kullawa Alummar, Wanda kuma,ba dai dai bane.
Ibrahim sani gama pyramid radio.