Maitaimakawa Gwamnan jihar kano Alh Abba Kabir Yusuf, a harkokin ciyar da yanmakaranta a fadin jihar kano, Malam Umar Musa Gama, ya jaddada kudirin ofishinsa na inganta harkokin ciyarwa a makarantun furaimare da sakandire a dukkannin kananan hukumomi 44 dake fadin jihar kano.
Malam Umar Musa Gama, ya bayyana haka ne a lokacin da aka rakashi ofishinsa domin kama aiki.
Yace, ofishinsa ba zai laminci irin mutane da suke sanya rashin gaskiya a cikin harkokin ciyar da dalibai ba,inda yace,ofishinsa ya zo da tsare_tsare da za su kara inganta harkokin ciyarwa yadda ya kamata.
Umar Musa Gama, ya nuna mutukar godiyarsa ga jagora DR.Rabiu Musa Kwankwaso da Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar kano, bisa gudunmawa da suke baiwa jamiyyar’ NNPP da Alummar jihar kano da kuma, cancanta da aka duba tare da bashi wannan matsayi domin ba da gudunmawa a fannin harkokin ilimi.
A jawabinsu daban_daban makusanta ga Umar Musa Gama, Abubakar Yahuza Gama da Alh.Mamman Nation da Shugaban jamiyyar NNPP na yankin Gwagwarwa da Alh. Abdulsalam Gama majidadin gidan Hon.Maggi da Alh. Mustapha mai Sikeli,Sun yi jawabinsu daya bayan daya dangane da wannan matsayi Umar Musa Gama ya rabauta da shi.
Alh.mamman Nation Wanda aka fi sani da