Press Statement
March 11th, 2023.
*BAN CE A ZABI WANI DAN TAKARA BA SAI ABBA KABIR YUSUF @Kawu Sumaila*
Zababben sanatan Kano ta Kudu, Hon. Suleiman Abdulrahman Kawu Sumaila ya bayyana cewar ba gaskiya ba ne jita-jitar da ke yawo cewar yana marawa wata jam’iyya baya a zaben gwamna da ke tafe.
Mataimaki na musamman ga Sanata Sumaila kan sabgar yada labarai, Abbas Adam Abbas, ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Kano.
Abbas yace wannan labari ba shi da tushe ballantana makama.
Ya bayyana cewa wasu masu neman tayar da zaune tsaye gami da yarfen siyasa ne ke yada wannan labari na bogi, inda yace a shirye su ke su dauki matakin shari’a kan duk mutumin da ke neman bata sunan Hon. Suleiman Abdul Rahman Kawu Sumaila
Yace Sanata Kawu Sumaila cikakken mai biyayya ne ga jam’iyyar NNPP da jagoranta Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, a don haka ba zai taba furta kalaman da ke nuni da a zabi wata jam’iyya ta daban ba a yayin zaben gwamna da na ‘yan majalisar jiha.
Abbas ya rawaito Sanata Kawu Sumaila na kira ga daukacin al’ummar jihar Kano da su zabi Abba Kabir Yusuf a matsayin gwamnan jihar Kano tare da sauran ‘yan takarar majalisar jiha a tutar jam’iyyar NNPP a zaben da zai gudana a ranar 18 ga watan Maris.