Mataimakin gwamnan jihar Jigawa, Malam Aminu Usman Yakubu, ya halarci bikin baje-kolin tattalin arziki da cinikayya na kasar China da Afirka karo na uku.
Taron wanda shine babban taro a cikin ukun ya gudana a birnin Changsha na lardin Hunan.
Kaza lika ya halarci wasu muhimman tarukan bukuwa, ciki har da dandalin tattaunawa kan inganta hadin-gwiwar kasar China da Afirka a fannin raya muhimman ababen more rayuwar al’umma, tare da gabatar da jawabi.