Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, wato Alhaji Aliko Dangote, ya sake zama wanda ya fi kowa kudi a Afrika kamar yadda shafin ƙididdigar masu kuɗi dake kasar Amurka Forbes ya wallafa.
Dangote dai ya ci gaba da zama na ɗaya a kuɗi a Afrika duk da irin faɗi tashin da ake samu a harkokin kasuwanci a cikin shekarun baya-bayan nan.
Dangote, wanda ya shahara a ɓangaren samar da siminti, shi kaɗai ne ɗan Najeriya da ya shiga jerin manyan masu kuɗin duniya 200.
An bayyana cewa Aliko Dangote da babban attajiri Johann Rupert ɗan ƙasar Afrika ta Kudu ne kaɗai suka shiga jerin masu kuɗin a nahiyar Afrika.
Yanzu haka Dangote na da tarin dukiya da aka ƙiyastata yawanta da dala biliyan 14.2 wacce ta ƙaru daga dala biliyan 12.1 da take a shekarar da ta gabata.
Shafin jaridar Forbes ya bayyana cewa karyewar hannayen jari da samun ƙaruwar kuɗaɗen ruwa na daga cikin abubuwan da suka yi ƙasa da masu kuɗi da yawa a shekarar 2023.