Miji ne ya ɗaga wayar matarsa cikin dare Kun San me ya faru kuwa ?
Yana ɗagawa kafin yayi magana kawai sai yaji muryar mahaifiyar matarshi ce tana ta faɗa tana cewa sai Kiranki ake yi bakya son ɗaga waya. Ki Saurareni sosai kiji abinda zan faɗa.
Mijin Yana Jin ta, dan ta hana shi magana.
Da farko Malam yace ki tabbata kinyi anfani da maganin da na kawo Miki daxu mijinki Yana Nan banyi Miki bayanin yadda zakiyi anfani dashi ba kuma dare yayi na tafi.
1. Na farar Leda:. Ki dinga saka Masa a shayinsa ko ki dafa dashi
2. Na ruwan Ki saka Masa a abincinsa
3. Na takardar ki zuba a bakin kofar dakinsa ya tsallaka in zai shiga daki.
4. Na farar takardar a rubuce Miki abinda ke jiki a tafin kafarki sannan idan ya kwanta ki tsallaka shi ki taka tumbinsa.
Idan har kinyi wannan yadda na fada Miki malam yace ko mahaifiyarsa da danginsa sai yadda kikayi dasu, Kuna Zaki mallake ki juya shi kamar yadda ake saka kwai akan faifai ko kwarya kina jutawa.
Komai kika ce Masa shi zaiyi ba zaiyi Miki musu ba,. Ni na gama nawa aikin ya rage naki sai da safe….
Sai ta kashe waya.
In Kaine mijin ya zakayi da uwar da matar