Gwamnan Jihar Kano Engr Abba Kabir Yusuf ya yiwa alkawarin cigaba da tura ɗalibai Masu hazaka zuwa kasashen waje domin karo karatu kamar yadda gwamnatin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ta gudanar a baya.
” A yayin jawabina bayan an rantsar da ni a matsayin gwamnan jihar kano na yi alkawarin zan cigaba da baiwa daliban da suka kammala karatunsu na digiri da kyakyawan sakamako damar zuwa jami’o’in kasashen waje domin yin digiri na biyu da na uku”.
Kadaura24 ta rawaito Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan ne a sashihin shafin sa na Facebook a safiyar ranar Asabar din nan.
Gwamnan ya bada tabbacin nan da wata mai kamawa za’a fara aikin tantance rukunin farko na daliban da za’a baiwa tallafin karatun zuwa daga na nan gida da na kasashen waje.
Hakazalika gwamnan yayi alkawarin sake bude makaranta kire-kire guda 47 da aka da su a jihar domin cigaba da gudanar da karatun.
” Mun kuma kudirci aniyar dawowa tare da sake bude makarantun koyar da al’amuran addinin musulunci guda 44 wadanda tsohon gwamnan kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya ƙirƙiro Kuma gwamnatin Ganduje ta rufe su.” A cewar Abba Gida-gida
Gwamnan ya kuma bada tabbacin za’a bude wadancan makarantu tare da fara bada gurbin karatu ga daliban da suka chanchanta.