Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun kai hari wasu ƙauyuka a jihar Zamfara, inda suka kashe mutane da dama tare da sace ƴan mata fiye da 30 a ƙaramar hukumar Maradun.
Sashin hausa na BBC ya wallafa cewa Maharan sun afka ƙauyukan Sakkiɗa da Janbako a jiya Asabar da rana inda suka kashe mutum sama da 20 a Sakkiɗa tare da jikkata karin wasu.
Wani mazaunin yankin ya shaida wa BBC cewa, an dauki ƴan mata fiye da 30 a kauyen Gora a yayin da suka tafi yin itace a dajin Ɗaggera.
Ya ce, “ƴan bindigar sun bayar da sanarwa tun kafin sace yaran cewa idan har muna so mu yi noma a Ɗaggera a bana, to sai mun zauna mun yi sulhu da su, kuma mu yi ta sulhu da su amma bamu san dalilin sace mana yaran ba.”
“ Har kawo yanzu dai bamu ji daga garesu a kan yaran ba, amma jami’an tsaro sun bi bayansu sai dai ba wani labari” inji shi.