Ana daukar matakai daban-daban a New Delhi, babban birnin kasar Indiya sakamakon karuwrar gurbatar iskar shaka.
Rahotannin da kafafen yada labarai na kasar suka fitar na nuni da cewa, kididdigar gurbacewar iska ta haura sama da kashi 470 cikin 500.
Hukumomin sun dauki matakai daban-daban na yaki da gurbatar iska.
A cikin matakan da aka dauka, an rufe masana’antu da wuraren gine-gine a birnin a yau, kuma an sanya takunkumi kan zirga-zirgar motoci masu aiki da diesel.
An kuma amsa kiran da mazauna birnin suka yi wa hukumomi na dakatar da makarantu.
An dakatar da zuwa makarantun firamare a Delhi da kuma iyakance wasu aiyuka a waje na makarantun sakandare.
A cikin sanarwar da gwamnatin ta fitar, an sanar da cewa idan wadannan matakan gurbatar iska ba su ragu ba, za a dauki tsauraran matakai a mako mai zuwa.