Rahotanni daga kasar Tanzaniya, na nuni da cewa wani jirgin sama mallakin kamfanin sufuri na Precision Air, ya yi hadari, inda ya fada tafkin Victoria dake yankin Bukoba na jihar Kagera.
Kafofin watsa labaran kasar sun ce ana shirin fara gudanar da ayyukan ceton wadanda ibtila’in ya rutsa da su.