Yayinda Dillalai masu hada Hadar kudaden kasashen waje suka Kai karar Hukumar EFCC wajen babban sifeton Yan sanda Najeriya saboda fara kama wasu daga cikin masu hada Hadar kudaden wajen da Kuma yadda EFCC din ta hanasu sakat akan batun karancin Dala Wanda ya biyo bayan sauyawa Naira Fasali ,Atiku Abubakar shi Kuma ya nemi a Sanya hoton Maigidansa Obasanjo akan sabbin takardun kudin da zasu fito Nan gaba .
Wani bincike ya gano cewa a yunkurin gwamnatin tarayya na sauyawa Naira Fasali tsakanin kwanaki biyar zuwa yau kayan masarufi da sauran kayayyaki sun fara tashin gauron zabi Sabida karancin Dala da Kuma gaggawar da Yan kasuwa keyi na saye kayayyaki Domin maye gurbinsu da tsofaffin kudaden Naira da suka Tara a gida ko kasuwa Dan gudun yin hasarar .
Kuna ganin Hakan shine mafita ga talakawan Najeriya da Kuma tattalin arzikin kasa ?
Yaya farashin kayayyaki da kayan masarufi suke a yankunanku yanzu ?