Rundunar yan sanda ta gargadi kungiyar NLC akan Zanga-zangar da zata gudanar

Muƙaddashin babban sufetan ƴan sanda na kasa, Kayode Adeolu Egbetokun ya bayana damuwa kan zanga-zangar da ƙungiyyin ƙadago suke shirya yi a duk fadin kasar, inda ya yi gargaɗin cewa rundunar ba za ta lamunci duk wani abu da zai kawo rikici ba.

Rundunar ƴan sandan ta ce a baya irin wannan zanga-zangar ta kan rikiɗe ta zama tashin hankali, saboda haka ta ke gargaɗin cewa ba za ta bari a gudanar da duk wani abu da zai kawo matsalar tsaro ba.

A wata Sanarwar da kakakin rundunar ƴan sandan Najeriya, ACP Olumuyiwa Adejobi ya fitar, rundunar ta ce ƴan ƙasa suna da ƴancin yin zanga-zanga kamar yadda kundin mulki ya yi tanadi, amma dole ne a gudanar da ita cikin kwanciyar hankali.

ACP Adejobi ya ce duk wani yunƙurin tayar da rikici a lokacin zanga-zangar ƙungiyar ƙwadago zai fuskanci fushin hukuma.

Ƙungiyoyin ƙwadago a Najeriya sun shirya fara zanga-zanga a faɗin ƙasar daga ranar Laraba 2 ga watan Agusta domin nuna rashin amincewa da soke tallafin mai da gwamnati ta yi.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments