Guda daga cikin ‘yayan shugaba Buhari ta fadi wasu kalamai akan mulkin Mahaifin ta

Yar shugaban kasa mai barin gado Hanan Muhammadu Buhari, an ji yo ta ta na yabo yadda mahaifin na su ya gudanar da mulkin sa na Zango biyu

Da ta ke magana a shafin ta na Instagram a ranar Talata, 23 ga watan Mayu 2023, Hanan ta jinjinawa kokarin shugaban kasa Buhari duk da tofin alatsine da wasu al’ummar kasar ke yi.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wannan Baiwar Allah ta wallafa hoton mahaifinta ya na kaddamar da jiragen ruwan yaki a Legas a makon nan da muke ciki wanda kuma shine mako na karshen waadin mulkin na sa.

Hanan ta rubuta ‘Mahaifi na…Wanda yasamu nasara a boye!” – Hanan Buhari

Hanan ta rubuta ‘Mahaifi na…Wanda yasamu nasara a boye!” – Hanan Buhari
Ayyukan gwamnatin Buhari Babu mamaki yadda shugaban kasar yake yawon kaddamar da ayyuka ne Hanan ta ke ganin mahaifinsu ya cancanci a yaba masa.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments