Kafar yada labaran China ta rawaito cewa akalla mutane 46 ne suka mutu lokacin da wata mummunar girgizar kasa ta afka wa kudu maso gabashin kasar.Girgizar kasar, mai karfin sama da maki shida, ta faru ne da misalin karfe daya na rana a agogon yankin Sichuan, ta kuma yi tafiyar kilomita 10 cikin kankanin lokaci.
Daga Walid Y Hari
Kafar yada labaran yankin ta rawaito cewa girgizar kasar ta shafi turakun sadarwa da haddasa zabtarewar kasa, da lalata gine-gine.
A makon jiya ne hukumomi suka gargadi mazauna babban birnin yankin Sinchuan, wato Chengdu su miliyan 21 su zauna a gida saboda barkewar cutar korona.
Har wa yau, hukumar da ke kula da ibtila’in girgizar kasa a China, ta ce inda girgizar ta fi shafa shi ne Lunding, wani gari da ke saman tsauni, mai nisan kilomita 226 daga Chengdu.
Gidan talbijin din CCTV ya rawaito cewa mutane 11 sun mutu a birnin Ya’an, yayin da wasu 22 suka mutu a makwabciyar yankin Ganzi.