Ana horas da malamai kan yadda za su yi wa’azi cikin tsafta a Jamhuriyar Nijar.

Kungiyar Jama’atul Kitabu Was-sunnah a Jamhuriyar Nijar ta fara wani zama na kwanaki bakwai da zummar karawa juna sani tsakanin malamai, da ba su horo kan dabarun yin wa’azi ba tare da amfani da kalamai ko lafuzan da ka iya ta da zaune tsaye ba.

Daga Walid Y Hari

Malaman da kungiyar ta gayyato daga wurare daban-daban, za su bai wa malaman jihohi 8 wannan horo, da nufin tsaftace harkokin wa’azi da abin da yta shafi addini a kasar.

Ana yawan korafi kan yadda wasu malamai ke zafafawa ko fadar abin da ya zo bakunansu lokutan wa’azi, inda kan tunzura mabiya har a samu barkewar tashin hankali tsakanin mabiya addinai daban-daban, ko ma wadanda ke cikin addinin guda.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments