Gwamnatin jihar kano ta bayyana matsayar ta akan batun da yake yawo dangane da gidan marayu na nassarawa wanda wasu mata biyu da suka kammala zamansu a gidan suka kitsa shi
kwamishinar mata da walwalar al’umma Dr Zah’ra’u muhd Umar ce ta bayyana hakan ga manema labarai inda tace matan biyu da suka dawo gidan da zama kowacce ta mallaki hankalinta kuma sunsamu kulawar data dace daga gwamnati inda guda daga cikinsu Mai suna Saudat ta ki zama a gidan mijinta ta baro ya’yanta uku ta dawo gidan da zama yayin da dayar maisuna Fatima (LADIDi) ta samu ilimi a fannin lafiya har gwamnati ta bata aikin yi amma dukkansu suka kasa duba gatan da akayi musu suke kulla manakisa kala kala wacce bata kyale ma,aikata da kananan yaran gidan Nassarawar ba.
kwamishinar tace bayan bincike da kwamitin da aka kafa ya fitar kuma gwamnati ta amince da subar gidan marayun na Nassarawa tun da doka tace daga shekaru goma sha takwas kowanna maraya zaibar gidan yaci gaba da rayuwarsa a wani wuri daban bayan an samar musu abinyi Wanda su LADIDi da Saudat duk sun samu wannan tagomashin sai dai sunce baza subar gidan ba
Malam kabiru zubairu guda daga cikin yan kwamitin daga ma,aikatar mata da walwalar al’umma yace zarge zargen da ake yadawa sun hadar da sakacin ma,aikatar mata akan bayar da yara ga masu bukatar su rainesu wanda yace akwai wakilan kwamatin da suka Kai Tara kafin bayar da yaro inda daga karshe in an amince kotu ce kadai zata damka yaron da ake bukatar a rikeshi a hannun wanda ya bukata bayan zurfafa bincike, ba kamar yadda akace ma,aikatar nayin son Rai ba.
Dr Zah’ra’u muhd Umar tace Kiran taron yan jaridun nada nasaba da yadda matan suke shiga kafafen yada labarai domin batawa ma,aikatar da gwamnati suna.