Maaikata 1699 sun rabauta da komawa bakin aiki Bayan Korar da gwamnatin da ta shude tayi a jihar Adamawa.
Solomon Kumanngar, shugaban washing Yada labarai na gwamna Adamawa Ahmad Fintiri shine ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a birnin Yola
Wadanda suka rabauta da komawa bakin aiki sun hada da malaman 699 da kuma maaikatan lafiya 1000.
A gefe guda kumangar, yace gwamna Fintiri ya kuma debi Karin maaikatan lafiya 1113 an rarraba su zuwa lungu da sako domin inganta fannin lafiya
Kazalika yace maaikatan gidan gwamnati da dama an rarraba musu offer.