An bayyana Samar da Tashar sufuri kayayyaki ta kasa , domin yin sufurin kayan yankasuwar jihar Kano da cewa.abin ci gaba ne da zai bunkasa tattalin arzikin jihar nan .
Shugaban matasa kuma, Mai rajin ci gaban alummar jihar Kano, a kungiyar kasuwar masu siyar da magunguna dake malam Kato a nan jihar Kano,Alh mamuda zangon kabo ne,ya bayyana Haka a zantawarsa da manema labarai a ofishinsa dake kasuwar.
Mamuda zangon kabo, yace,bude wannan Tasha zai taimaka wajen Samarwa matasa ayyukan yi,musamman a halin da alumma suke tsinci kansu a ciki da habakar tattalin arzikin kasuwancin jihar Kano,inda yace, jihar Kano cibiya ce ta kasuwanci ana alfahari da ita a dukkannin kasashen ketare.
Zangon kabo, Ya shawarci yankasuwa na gida da na ketare da suzo jihar Kano domin zuba jari domin yin kasuwanci, kasancewar akwai kasuwanni da suke da yawan alumma.
Haka zalika, Ya bukaci Gwamnatin tarayya data kara bijiro da irin wadannan tashoshi duba da yadda suke taimakawa wajen bunkasar tattalin arzikin kasuwanci da Samar da hanyoyin samun kudaden haraji da Samar da ayyukan yi ga yankasa.yace,jihohi da dama a kasar nan irin wadannan tashoshi suna taka rawar gani na farfado da bunkasa tattalin arziki ta kawanne Fanni.
Daga karshe ya taya alummar musulmi murnar zagayowar sabuwar shekarar musulunci, inda ya bukaci alummar kasarnan da su taimakawa kasar nan da addu,oin samun zaman Lafiya mai dorewa duba da halin da alummar Najeriya suka tsinci kansu a ciki musamman yadda lamarin Matsalar tsaro ta samu kanta a ciki.
Ibrahim Sani Gama.