Abdullahi Umar Ganduje ya sa labule da Anyim Pius Anyim a gidansa da ke birnin tarayya Abuja
Zuwa yanzu ba a san abin da shugaban na APC ya tattauna da tsohon sakataren gwamnatin kasar ba
Dr. Ganduje ya sha alwashin karfafa jam’iyya mai mulki yayin da aka gagara gane manufar Anyim
Wasu su na ganin akwai yiwuwar Sanata Pius Anyim ya sauya-sheka daga PDP musamman ganin take-takensa a ‘yan kwanakin bayan nan
Za a iya tuna cewa tsohon shugaban majalisar dattawan ya ziyarci Mai girma shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadar sa a kwanakin baya.
Yayin ziyarar, Olisa Metuh ya na tare da Anyim wanda ya rike matsayin sakataren gwamnatin tarayya a gwamnatin Dr. Goodluck Jonathan.