Yan bindiga sun yi awon gaba da wani Basarake da matar sa

Yan bindiga dauke da muggan makamai sun yi awon gaba da basaraken garin Gurku a karamar hukumar Karu ta jihar Nasarawa

Maharan sun sace Jibril Mamman Waziri da matarsa, Sa’adatu Waziri a daren ranar Lahadi, 6 ga watan Agusta

Kakakin rundunar yan sandan jihar, DSP Ramhan Nansel, ya tabbatar da lamarin a ranar Litinin, 7 ga watan Agusta. Ya ce:

Cikin lafazi kakakin rundunar yace “Ina mai son tabbatar da cewar da misalin karfe 10 na daren ranar 6 ga watan Agusta, rundunar yan sandan jihar Nasarawa ta samu kira mai cike da damuwa cewa yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun farmaki basaraken Gurku, da ke kimanin kilomita 10 daga ainahin garin Mararaba.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments