Mutane 2 ne suka jikkata sakamakon fashewar wata mota dauke da bama-bamai a Mogadishu, babban birnin Somaliya.
A gundumar Trepiano da ke babban birnin kasar, bama-baman da aka sanya kan wata mota sun fashe.
An rufe hanyoyin da ke zuwa yankin bayan fashewar.
An kuma ji karar fashewar bam din daga sassa daban-daban na birnin.
An rawaito cewa an nufi wani ma’aikacin ofishin ‘yan sanda yayin kai harin kuma wasu mutane 2 da ke wucewa sun jikkata a lokacin da bam din ya fashe.
Har yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin kai harin.
Kungiyar ta’adda ta Al-Shabaab na ci gaba da kai hare-haren bam kan matsugunan fararen