Gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da sake bude makarantu 45 daga cikin 75 da ta garkame a shekarar da ta gabata.
Sakataren ma’aikatar ilimin jihar, Alhaji Kabiru Attahiru ne ya sanar da hakan a ranar Laraba yayin da ya karbi wasu baki a ma’aikatar sa
Attahiru ya bayyana cewa, kalubalen tsaro ya yi kasa a jihar shiyasa aka bude makarantun amma sauran 30 din an bar su a rufe ne har sai an ga abinda hali yayi
Gwamnatin jihar ta Umarci rufe makarantun a watan Satumban 2021 bayan an sace daliban Makarantar gwamnati ta jeka ka dawo dake Kaya a karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara.
“A yayin bude makarantun, mun rarrabe su zuwa kashi uku, Koraye, dorawa da ja.
“Koraye sune na yankunan da babu wani kalubalen tsaro, dorawa sune makarantun da ke inda akwai kalubalen tsaro amma kadan, sai jajaye sune a yankunan dake da manyan kalubalen tsaro.”
Attahiru yayi bayani. Yace dukkan makarantun 75 sun fada kashin ja a lokacin da aka rufe su kuma hatsarin ne yasa aka cigaba da barinsu a rufe.
“A yau ina farin cikin sanar muku cewa sakamakon cigaban da aka samu a fannin tsaro a jihar, mun sake bude wasu makarantu 45 daga cikin 75 yayin da sauran 30 din zasu kasance a rufe.