An ceto mutumin da ya kwashe shekara 20 a kulle a Kaduna.
Daga Walid Hari.
Rundunar ƴansandan Najeriya reshen jihar Kaduna ta ƙaddamar da bincike kan dalilan da suka sanya aka kulle wani mutum a cikin ɗaki na tsawon shekara 20.
A ranar Laraba ne ƴansandan suka ceto mutumin mai suna Ibrahim Ado, mai kimanin shekara 67 a wani yanki na birnin Kaduna da ake kira Bayajida.
Mai magana da yawun rundunar ƴansanda a jihar Kaduna ASP Muhammed Jalige, ya ce jami’an rundunar sun kai samame a gidan da aka kulle mutumin ne bayan samun bayanan sirri.
Ya ce mutumin mai kimanin shekara 67 ya kwashe tsawon shekarun ne yana garƙame a ɗakin, inda a nan yake cin abinci da kuma duk lamurransa.,, kuma an same shi cikin mummunan yanayi.