Fargabar Hari: Bayan Jabi Lake Mall, Wani Babban Kamfani Ya Sake Rufe Ayyukansa A Abuja.
Kamfanin gine-gine na Julius Berger ya rufe ayyukansa a babban birnin tarayya Abuja.
Rufewar na zuwa ne bayan martani kan fargabar harin ta’addanci a babban birnin tarayya da tsakiyar Abuja.
A cikin sanarwar da kamfanin ya fitar a ranar Asabar, ya shawarci ma’aikatansa su guji zuwa wuraren taruwar mutane a yayin hutun karshen mako.
Sanarwar tace za ta duba yiwuwar yin kaura na wucin gadi zuwa wasu wuraren.
“Ana bada shawawar a kaurace wa wuraren taruka a Abuja da kewaye, ciki har da kanti, wuraren cin abinci,da kulob da wasu wurare da mutane ke taruwa