Sheikh Ahmad Gumi ya caccaki kokarin babban bankin Najeriya na sauya wasu takardun Naira inda ya kwatanta lamarin da halaka kai ta fannin tattalin arzikin ‘yan Najeriya balle mazauna kauye.
Kamar yadda yace, kashi 80 na ‘yan Najeriya mazauna kauye ne kuma sun dogara da tsabar kudi domin siye da siyarwa.
Gumi yace duk wani tsari da zai mitsike zagayawar kudi tsabarsu zai zama tamkar ibtila’i ga kasar. Ya kara da yin bayanin cewa tsarin ba zai taba hana masu garkuwa da mutane kudi tsabarsu ba saboda zasu iya yanke hukuncin karbar kudin fansa a dala da sauran kudaden ketare kuma hakan ya matsantawa rayuwar jama’a.