Messi zai bar PSG, Ronaldo zai tafi Saudiyya.

Daga Walid Hari

Lionel Messi, ya shirya barin Paris St-Germain a bazara, kasancewar ba zai yarda da wani tayi na sabunta kwantiraginsa a kungiyar ta Faransa ba. (Beteve, via Star)

Ya kamata matashin dan wasan tsakiya na Ingila Jude Bellingham, mai shekaru 19, ya je Manchester United idan ya bar Borussia Dortmund, a shawarar tsohon mai tsaron raga a Old Trafford Ben Foster. (Metro)

Kungiyar Al Hilal ta Saudiyya ta ce Cristiano Ronaldo, na sha’awar komawa wurinta a bazara. (Mirror)

Tsohon kociyan Tottenham da Paris St-Germain Mauricio Pochettino, wanda ake rade-radin Ingila za ta dauka, ya halarci wasan da Ingila ta yi canjaras da Jamus 3-3 a Wembley. (Telegraph – subscription required)

Newcastle na sa ido a kan matashin dan wasan tsakiya na Brazil Andrey Santos, mai shekara 18, wanda ke taka leda a Vasco da Gama. (Fabrizio Romano)

Chelsea ta kori mai horas da ‘yan wasanta bangaren guje-guje da tsalle-tsalle Thierry Laurent, jami’I na hudu da ta sallama.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments