Shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan ya ce, “Wadanda ke goyon bayan kungiyar ta’addanci da sunan yaki da DAESH suna da alhakin duk digon jinin da aka zubar.”
Shugaba Erdogan ya gudanar da taron manema labarai a cibiyar yada labarai bayan taron kolin shugabannin kasashen G20 da aka gudanar a Indonesiya.
Dangane da harin ta’addancin da aka kai a birnin Istanbul, Shugaba Erdogan ya bayyana cewa wadanda ke goyon bayan kungiyar ta’addanci da sunan yaki da DAESH, na da alhakin duk digon jinin da aka zubar.
Ya ce, “Muna sa ran goyon bayan gaske daga dukkan abokanmu da kawayenmu kan gwagwarmayar Türkiye na adalci.”
Shugaba Erdogan ya ce, Türkiye za ta ci gaba da aiwatar da dabarunta na kawar da barazanar ta’addanci daga tushenta.
Ya ce, “Tare da duk abun da za su yi, da ko wanene ke goya musa baya, ‘yan ta’adda ba za su iya kubuta daga mummunan makomar da ke jiran su ba.”
Shugaba Erdogan, ya ce, “Ina kara jaddada cewa babu wurin aikata duk wani nau’in ta’addanci a makomar kasarmu da yankinmu.”
Erdogan, game da samun F-16 daga Amurka, ya ce, “Shugaban Amurka, Joe Biden ya ce akwai ci gaba mai kyau.”
Dangane da Jamhuriyar Turkawan Arewacin Cyprus a matsayin mamba mai sanya ido a Kungiyar Kasashen Turkawa, Erdogan ya ce, “Babu bukatar mu samu izini daga kowane wuri, daga kowace kasa game da wannan shawarar. Wannan aikin an riga an gama shi.”
Shugaba Erdogan ya kuma yi magana game da makamai masu linzami da suka fada a Poland, ya ce, “Dole ne in mutunta sanarwar da Rasha ta fitar, yana da muhimmanci a gare mu cewa Rasha ta bayyana cewa, ‘Wannan ba shi da alaka da mu.’”
Erdogan ya ce, “Yayin da muke kokarin tattara Rasha da Yukren a kan teburi guda, babu bukatar gano ko cire abokin tarayya na uku na wannan yakin.”
Shugaba Erdogan game da jigilar hatsi ya ce, “Tattaunawarmu tana ci gaba da gudana kuma na yi imanin cewa abubuwa za su ci gaba da kasancewa yadda suke a halin yanzu, ba tare da wata matsala ba. Za mu tattauna batun jigilar taki da ammoniya da Shugaban Rasha, Vladimir Putin. Za mu yi kokarin kara tsawon lokacin yarjejeniyar zuwa shekara 1.”