Ana ci gaba da tattaunawa tsakanin dan wasan tsakiya na Ingila Mason Mount da masu kungiyar Chelsea, a kan kwantiragi, kuma bayanai sun nuna cewa an cimma nasara a ‘yan makonnin da suka gabata.
Bayanin Eden Hazard cewa watakila ya bar Real Madrid a watan Janairu zai dadada wa Newcastle United, kungiyar da a baya ake cewa dan wasan na tsakiya na Belgium zai koma can.
Shugaban Sporting Lisbon Frederico Varandas ya musanta rahotannin da ke cewa Cristiano Ronaldo, zai koma can, inda ya ce ba su yi wata magana mai kama da haka ba.
An cire hotunan Ronaldo daga jikin bangon filin wasa na Manchester United, Old Trafford ranar Laraba, ‘yan sa’o’i kafin a yada hirar da dan wasan ya yi da Piers Morgan.
Dan wasan tsakiya na Faransa Adrien Rabiot, ya ce ya yi sa’a da bai bar Juventus ya koma Manchester United ba a lokacin bazara.
Matashin dan wasan da Chelsea ke hari Endrick, ya ce yana shirin tafiya wata kungiya da za ta buga gasar Zakarun Turai, kuma tuni dan Brazil din mai shekara 16 wanda manyan kungiyoyin Turai ke zawarcinsa daga Palmeiras ya fara koyon Ingilishi.
Shugaban Barcelona Joan Laporta ya ce kungiyar ta so sayen dan gaban Colombia Luis Diaz, kafin Liverpool ta dauke shi daga Porto.
Barcelona na son matashin dan wasan tsakiya na Arsenal Charlie Patino, mai shekara 19, da ke zaman aro yanzu a Blackpool, kuma kwantiraginsa zai kare a bazara mai zuwa.
Shakhtar Donetsk na son yuro miliyan 100 ( fan miliyan 87.75) a kan dan wasanta na gaba na gefe Mykhaylo Mudryk, dan Ukraine, mai shekara 21, wanda kungiyoyi da dama da suka hada da Arsenal da Manchester City da Newcastle United ke so.
Tsohon dan bayan Argentina Martín Demichelis, mai shekara 41, wanda ya yi shekara uku a Manchester City, ya bar aikin horarwa a Bayern Munich domin zama sabon kocin kungiyar River Plate ta Arg entina.