Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta bukaci Godswill Akpabio ya mika kan sa a hedikwatarta domin bincikar sa.
Jaridar Premium Times, tace an ji Sanata Godswill Akpabio zai amsa tambayoyi a kan zargin rashin gakiya da EFCC ta ke yi masa.
Hukumar ta bukaci Sanata Akpabio ya mika kan shi da kan shi a ranar 9 ga Mayu.
Kazalika jaridar Sahara Reporters ta ce tsohon Ministan harkokin Neja Delta yana cikin manyan masu neman zama shugaban majalisar dattawa a karkashin APC.
 Wannan umarni ya na cikin wata wasika da hukumar ta aikawa tsohon Gwamnan na Akwa Ibom ta hannun Lauyansa, Umeh Kalu, SAN.
Godswill Akpabio bai da lafiya? Da aka rubutawa Akpabio takarda irin haka a watan Maris, sai ya maida amsa ta bakin Lauyansa da ba zai samu zuwa ba domin zai je asibitin kasar waje.