Arewa ce ta cancanci samar da shugaban majalisar dattawa sanata–Abdul Aziz Yari

Tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma zababben sanata, Abdul’Aziz Yari, ya bukaci jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da ta duba kokari wajen rabon mukamai a majalisa ta 10 ba tare da la’akari da kabilanci ko addini ba.

Yari ya bayyana hakan ne jim kadan bayan ganawar sa da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a villa da ke Abuja.

Ina shawartan jam’iyyar APC da cewa su yi kokari wajen rabon mukamai ba wai addini ba. Saboda addini baya cikin kundin tsarin mulkin Najeriya, kuma baya cikin manufofi da kundin tsarin mulkinmu.”

Arewa ta cancanci samar da shugaban majalisar dattawa, Yari, wanda ya kasance daya daga cikin zababbun sanatocin da ke neman shugabancin majalisar dattawa, ya bayyana cewa arewa ce ta fi bayar da kuri’u don tabbatar da nasarar APC a zaben shugaban kasa da ya gabata.

Saboda haka, ya ce ya kamata a ba yankin daman samar da shugaban majalisar dattawa na gaba.

“Kowa ya san rawar ganin da muka taka, duk da kasancewar sauran mutane na tunanin muna da namu. Amma mun zabi jam’iyya wacce ta ba APC damar sake kwace kujerar shugabanci.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments