Duk masu kudin garinmu sun yi hijira saboda rashin tsaro: wani matashi a jihar katsina

Daga Walid Hari.
Al’umar jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya sun bayyana yadda matsalar rashin tsaro ke ci gaba da addabar sassa da dama na jihar sakamakon ayyukan ‘yan bindiga, wadanda ke cin karensu babu babbaka a yankin.

Akwai tarin matsaloli masu dimbin yawa da rashin tsaro ya haifar wa jihar Katsina, kama wasu matsalolin za su dade suna yi wa cigaban jihar tarnaki, domin kuwa za a dauki lokaci mai yawa kafin a shawo kansu.

Ayyukan ‘yan bindiga sun tilasta rufe makarantu a wasu sassan jihar Katsina, bayan kai hari makarantar sakandiren Kankara tare da sace dalibai masu yawa, inda gwamnatin jihar ta rufe makarantun sakandire da na firamare zuwa wasu watanni kafin daga bisani a sake bude su.

Wata babbar matsala da ayyaukan ‘yan bindiga suka haddasa a jihar Katsina da ma wasu sassan arewacin Najeriya da ke fama da matsalar tsaro, ita ce hana manoma zuwa gonakinsu domin yin noma.
Da fatan Allah ya kawo gyara cikin lamarin.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments