Shi dai wannan Dan tahaliki mai suna Alfa Rafi’u mazaunin unguwar Abayawo dake karamar hukumar Ilorin ta yamma ya shiga komar jamian tsaro ne bayan samun sa da laifin yin bulunbukui bayan da ya ga kararrawar zunzurutun kudi har Naira miliyan 280.
A cewar jaridar DailyTrust Rafi’u bayan samun wadannan kudade bayyi wata wata ba sai ya fara gudanar da kara’in rayuwa ta hanyar siyen motocin hawa da Gidaje da kuma biyan kujerun ummura ga wasu na kusa da shi.
Bayan samun yakini akan cewa wannan Dan tahaliki ba zai dawo da wadancan kudade da suka shiga asusun sa ta hanyar kuskure ba tuni Bankin da hakan ta faru da shi ya hada hannu da jami’an tsaro na rundunar yan sanda ta kasa reshen jihar Kwara wajen ganin ya samu an yo masa dawayya da wadancan ya matsabbai na sa
Kai Kukah nasa rundunar yan sanda ke da wuya tuni suka bi dare suka bi rana har sai da suka cika hannu da Malam Rafi’u kamar yadda jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar Kwara SP Ajayi Okasanmi ya tabbatar wa manema labarai