Daga Walid Hari.
Rahoton ya bayyana cewa, kudaden da gwamnati ta ware don ciyar da dalibai a wadannan makarantu da babu su sun fada aljihun wasu mahandama, inji kwamitin ma’aikatar jin kai karkashin Mallam Abdullahi Usman.
A cewar Usman a lokacin da yake bayyanawa gwamnan Nasarawa Abdullahi Sule badakalar dake tattare da shirin a ranar Lahadi 16 ga watan Oktoba, ya ce jihar na gab da fita daga jerin jihohin dake cin gajiyar shirin.
Ya kuma bayyana cewa, tuni aka dakatar da ofishin tafiyar da shirin tare da maye gurbin jami’an dake kula dashi a jihar.
Hakazalika, hadimin na ministar jin kai ya ce, manya a ma’aikatar dama sun nemi a cire Nasarawa daga jerin jihohin dake cin gajiyar shirin.
Akalla makarantun firamare 1,203 ke cin gajiyar shiri.
Daga karshe ya mika godiya ga hukumar wayar da kan jama’a (NOA) da kuma shirin bautar kasa na NYSC wajen taimakawa a gani badakalar.