Dan wasan Ajax ya rasa ransa bayan gajeriyar jinya

Dan wasan kasar Jamhuriyar Congo Jody Lukoki da ya fara buga kwallon kafa ajin kwararru daga kungiyar Ajax ya mutu yana da shekaru 29.

Bayanan da jaridu da dama suka ruwaito ciki har da Jaridar Het Parool da ke kasar Netherlands, sun ce kafin mutuwarsa, Lukoki yayi fama da ciwon zuciya ne a wani asibiti da ke garin Almere, sakamakon dukan kawo wukar da wasu ‘yan uwansa suka lakada masa, a dalilin wata takaddama da suka yi.

Kungiya ta karshe da Lukoki ya bugawa itace ta FC Twente da ke kasar Holland ko Netherlands, wadda ya kulla yarjejeniya da ita a cikin watan Yunin da ya gabata, sai dai tun daga waccan lokacin bai samu bugawa kungiyar wasa ba, saboda mummunan raunin da ya ji a gwiwarsa, yayin da yake atisayen sharar fage.

Kafin kulla yarjejeniya da FC Twente, daga cikin kungiyoyin da Lukoki ya bugawa akwai Ajax, da SC Cambuur, da kuma Yeni Malatyaspor.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments