Kungiyar malaman makaranta ta kwalejin Kimiyya da fasaha ta Usaini Adamu dake Kazaure ta zabi Sabbin Shuwaganni.
Zaben wanda ya gudana a harabar Kwalejin, an gudanar da shi bisa kyakkyawan tsari da tanadi.
Dr Abdul’aziz Ibarhaim Gwadabe wanda ya lashe zaben a matsayin Shugaba ya bayyana godiyarsa ga Allah bisa samun wannan nasara tare da shan alwashin aiki kafada kafada da saura Shuwaganni domin ciyar da kungiyar gaba.
Ya kara da cewa wannan nasara ba tasa bace shi kadai nasara ce da ta shafi dukkanin mambobin Kungiyar, Musamman la’akari da cewar tun a baya an Samu nasarori da dama.
Dr Gwadabe yace wannan zaben zabe ne da ya samu nasara karo na biyu kuma jajurcewa sa da aiki tukuru mambobin suka kalla, suka sake zabarsa domin bashi damar cigaba da ayyukan ciyar da kungiyar gaba.
Daga cikin nasarori da suka samu a baya sun hada da kulla kyakkyawan Alaka da samar da Gidauniya ta Musamman don kyautata rayuwar malaman. Da kuma hakai kai da sauran hukumomi irin su NITDA don samun horo na Musamman don kyautata tsarin aiki
Dr Abdul’aziz yayi kira ga wadanda basu samu nasarar wannan kujera ba da su hada kai domin cigaba da samun nasara yadda ya kamata.