Shugaban kasar Aljeriya Abdulmadjid Tebboune, ya bayyana farin cikinsa da godiya ga mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero bisa gayyatar da aka yi musu na halartar taron kasa da kasa kan rayuwa da zamanin Imam Al-Maghili.
Shugaban kasar Abdulmadjid ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR CNOL, a fadar shugaban kasa da ke babban birnin kasar Algiers, ya lura cewa dangantakar kasarsa da Najeriya ta ginu ne a kan kwararan hujjoji na tarihi. Bakin Imam Al-Maghili Zuwa Kano.
Shugaba Tebboune ya bayyana aniyarsa na tallafawa duk wani shiri da zai inganta hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu musamman ta hanyar kasuwanci da musayar ilimi.
Ya yi alkawarin tabbatar da wata sabuwar hulda tsakanin ‘yan kasuwar Aljeriya da takwarorinsu na Kano, ya kuma yi kira ga kasashen Najeriya, Afirka ta Kudu da Aljeriya da su hada kai a kan batutuwan da suka shafi Afirka.
Shugaban ya dauki nauyin baiwa daliban Najeriya karin guraben karo karatu a fannonin Shari’a, Kimiyya da Koyan Sana’a.
Har ila yau, ya bayar da samar da ababen more rayuwa na musamman don horar da Limamai da malaman addinin Musulunci na Nijeriya har zuwa matakin digiri na biyu, ya kuma lura da cewa ziyarar mai martaba Sarkin Bayero ita ce mafarin sabon zamani a dangantaka tsakanin Aljeriya, Kano da Nijeriya musamman ma.
Tun da farko, Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR, ya tuna cewa dogon tarihin da ke tsakanin Kano da Aljeriya wanda za a iya danganta shi da ziyarar babban malamin addinin Musulunci kuma masanin falsafa dan kasar Aljeriya Imam Abdurrahman Al-Maghili a Kano a karni na 15.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana cewa tun a wancan lokaci ziyarar ta bullo da sabbin hanyoyin hadin gwiwa tsakanin Kano da Aljeriya.
Ya ce, lokacin cinikin da ake yi tsakanin sahara wani lokaci ne da ya inganta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da ta wanzu har zuwa yau.
Sarkin ya ci gaba da cewa, diflomasiyya ta zamani tana da tasiri mai kyau a kan waccan dangantakar ta tarihi, sannan ya kuma yabawa gwamnatocin biyu bisa gagarumin kokarin da suka yi wajen gudanar da manyan ayyuka da za su amfanar da yankunan biyu.
Sarkin Bayero ya bayyana godiya ta musamman ga shugaban kasar Aljeriya bisa tallafin tallafin karatu ga daliban Najeriya da kuma sauran tsare-tsare masu dimbin yawa da za su samar da kyakykyawan dangantaka a tsakanin kasashen biyu.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya kuma yi kira ga shugaban kasa da ya goyi bayan sha’awar sa na samun hadin gwiwa ta musamman tsakanin jiga-jigan ‘yan kasuwar Kano da takwarorinsu na Aljeriya tare da baiwa daliban Najeriya tallafin karatu don ci gaba da karatunsu a Aljeriya.
A yayin ziyarar mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero tare da rakiyar jakadiyar Najeriya a kasar Aljeriya, Hajiya Aisha Muhammad Garba, Alh. Ahmed Ado Bayero, Sarkin Dawkin Tsakar-Gida da Hakimin Kumbotso, Amb. Ahmed Umar, OON, Dan Malikin Kano, Mal. Magaji Galadima, Kachallan Kano da Mal. Isa Bayero, mataimaki na musamman ga mai martaba da sauran mataimaka.
Sa hannu
Abubakar Balarabe Kofar Naisa
Babban Sakataren Yada Labarai na Masarautar Kano, Jihar Kano.