Maitamakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ce yana neman afuwar al’ummar Musulmi bisa wasu kalamai da ya yi game da zaɓen shugabannin majalisar dokokin Najeriya.
A cewarsa ba a fahimci maganar a muhallinta ba, kuma ba shi da wata manufa na ɓata sunan addininsa.
Sanata Kashim a tattaunawarsa da BBC ya ce ya yi waɗannnan kalamai ne saboda maslahar Najeriya, ganin cewa suna da wasu bayanan sirri da bai dace ya fito bainar jama’a yana bayani a kansu ba.
Sannan yadda lamura ke tafiya a Najeriya a wannan lokaci, dole shugabanni su fito su ja hankali domin wanzuwar ƙasar baki-ɗaya.