Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP, Engineer Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi wata ganawa da zaɓaɓɓen shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu a birnin Paris.
Bayanai sun nuna cewa mutanen biyu sun shafe sa’o’i da dama suna tattaunawar.
Wata majiya da ba ta son a ambace ta, ta tabbatar wa manema labarai da ganawar a ƙasar Faransa.
Kwankwaso, wanda shi ne tsohon gwamnan jihar Kano ya zo na huɗu a cikin ƴan takarar shugaban ƙasa na 2023, inda ya samu ƙuri’u 1,496,687.
Duk da cewa babu cikakken bayani kan abin da tattaunawar ta ƙunsa, amma ana ganin cewa ba za ta rasa nasaba da shirye-shiryen kafa sabuwar gwamnati da za a rantsar a ranar 29 ga watan Mayu ba.
Bola Tinubu, wanda tsohon gwamnan jihar Legas ne kuma ɗaya daga cikin waɗanda ake wa kallon ƙwararru a siyasar Najeriya, har yanzu bai yi bayani dalla-dalla kan yadda gwamnatinsa za ta kasance ba.
A halin da ake ciki, zaɓaɓɓen shugaban ƙasar, Bola Tinubu na ƙoƙari ne wajen ganin ya shirya yadda zai karɓi mulki ranar 29 ga watan Mayu.
A ranar Laraba 10 ga watan Mayu ne zaɓaɓɓen shugaban ƙasar ya bayyana cewa zai tafi wata ziyarar aiki a ƙasashen Turai.