Wani gwamna yace ba zai mika mulki ranar 29 May ba

Samuel Ortom, gwamnan jihar Benue ya bayyana cewa zai miƙa mulki ga zaɓaɓɓen gwamnan jihar a ranar 28 ga watan Mayu, kwana guda kafin ranar da kundin tsarin mulki ya tanada domin miƙa mulki.

A cewar rahoton Tribune, gwamnan ya bayyana hakan ne a wajen taron majalisar zartaswar jihar, wanda aka gudanar a birnin Makurdi, babban birnin jihar a ranar Talata, 16 ga watan Mayun 2023.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa ba zai bar jihar ba, bayan ya miƙa mulki ga zaɓaɓɓen gwamnan jihar, Rev. Fr. Hyacinth Alia, cewar rahoton Vanguard.

Alia, ɗan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ya lallasa ɗan takarar Ortom da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaɓen gwamnan jihar na ranar 19 ga watan Maris, 2023.

Kwamishinan watsa labarai, al’adu da yawon buɗe ido na jihar, Michael Inalegwu, shine ya bayyana aniyar gwamnan ta ƙin barin jihar, jim kaɗan bayan an kammala taron majalisar zartaswar jihar ranar Talata.

Ortom ya karrama tsohon soja Gwamna Ortom ya tuna da wani babban ƙusa a jihar, inda ya karrama Manjo Gideon Orkar, ta hanyar sanya wa wata hanya mai tsawon kilomita 9 sunansa.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments