Bayanai na nuni da cewa cikin sa’o’I 48 hare-haren ‘yan ta’adda na jihar filato ya kashe kimanin mutanen da yawansu ya haura 100 a wasu sassa na jihar dai dai lokacin da gwamnatin jihar ta sanya dokar takaita walwalar jama’a a yankunan da hare-haren ke faruwa.
Dan Majalisar tarayya mai wakiltar Mangu da Bokkos Solomon Maren yayin jawabinsa gaban zauren majalisar a jiya laraba, inda ya ce mahara na ci gaba da kai hare-hare kan kauyuka tare da kisan mutanen da basu ji ba basu gani ba.
Maren, ya bayyana cewa hare-haren sun fi tsananta a yankin da ya ke wakilta wanda ke nuna matsananciyar bukatar daukar mataki duba da yadda mutanen kauyukan da ake kai hare-haren ke rayuwa cike da fargaba.
Dan Majalisar ya bayyana cewa cikin sa’o’I 48 sai da hare-haren ya kashe mutane fiye da 100.
Alkaluma sun nuna cewa mutanen da suka mutu yawansu ya haura 200 a irin makamantan hare-haren cikin watanni biyu da suka gabata a cewar Maren
A cewar Maren maharan na kone gidaje da gonaki har ma da shagunan da ake adana amfanin gona yana mai kakkausar suka ga matakan da gwamnati ke dauka a kokarin yaki da matsalar tsaron da yankuna da dama ke fama da shi a kasar nan .
Mu dai namu Addu’a ce Allah ya shiga tsakani nagari da mugu karshen rahoton kenan khadija wane zare da Abawa