A safiyar wannan rana ne daliban makarantar usman bun affan academy dake dake unguwar medile ta karamar hukumar kumbotso su sha tara mata goma maza tara ne suka samu ikon sauke Al’ku’ani mai girma.
A nasa jawabin shugaban makarantar malam umar abubakar wurno ya bayyana tarihin kafuwar makarantar inda yace makarantar ta fara da dalibai tara inda a yanzu take da dalibai sama da dari uku.
Wurno yayi kira ga iyayen yara dasu kara zage dantse wajan tallafawa karatun addini duba da cewar shine tabbas duk wani karatu ya biyu bayan na sanin Allah s.w.a
A nashi jawabin Alhaji zakariyya bin usman dake unguwar beci yayi kira ga masu iko dasu dinga taimakawa addinin Allah ta hanyar da Allah ya basu iko ya kuma yabawa malaman wannan makaranta bisa wannan babban aiki da suke na ilimantar da Al’umma
A nasu bangara wasu daga cikin daliban rukayya sagir da isa zakariyya sune suka bayyana irin nasu farin cikin tare da godewa Allah daya basu wannan baiwa daliban dai sun godewa iyayen su da malaman su bisa gudummawa da suka basu