Ofishin jakadancin kasar China dake kasar Koriya ta Kudu, ya tabbatar da mutuwar mutane hudu yan asalin kana wasu biyu sun jikkata, yayin wani turmutsitsi da ya abku jiya da dare a unguwar Itaewon dake birnin Seoul, fadar mulkin kasar, lokacin bukukuwan cika ciki ko Halloween a turance.
Ofishin jakadancin kasar Sin ya bayyana cewa, jim kadan bayan faruwar lamarin nan take ya kunna tsari na ba da agajin gaggawa, inda ya tuntubi bangaren Koriya ta Kudu cikin dare, domin sanin musabbin hadarin da kuma ‘yan kasashen waje da lamarin ya shafa, kana ya mayar da hankali matuka kan shafukan Intanet da na sada zumunta, don ganin ko akwai wani Basine dake neman taimako.
Ofishin jakadancin ya kuma mika ta’aziyarsa tare da aniyar taimakawa iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su yadda ya kamata. A cewar hukumomin ‘yan kwana-kwana na kasar Koriya ta Kudu, ya zuwa karfe 9 na safiyar yau agogon kasar, lamarin ya yi sanadiyar mutuwar mutane 151 kana 82 sun jikkata