Wata mazauniyar burnin tarayya Abuje dake faɗi tashin zama uwa tana neman kyakkyawan mutumin da zai iya sanya wa ta ɗauki ciki. Tauraruwar mai amfani da kafar sada zumunta, Uwaoma Susan Joseph, ita ce ta bayyana bukatar matar a dandalin Facebook tare da sakaya bayanan matar.
Yayin da matar mai kuɗi ta shirya biyan duƙ wanda ya ci sa’ar gama wannan aikin Naira Miliyan N3m, ta kuma kafa wasu sharuɗɗa yayin gudanar da lamarin.
Susan ta bayyana cewa matar tace duk wanda zai aikin za’a ɗaure masa ido lokacin da zasu sadu. Kuma zata rike shi har sai an tabbatar da ta samu juna biyu. Babban dalilin da yasa za’a ɗaure wa mutumin ido shi ne don kar nan gaba ya dawo yana nemanta da ɗansa. cewar Susan.