Daga hukumar EFCC guda daga cikin gwamnonin arewa ya amsa kira

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arziki ta’annati ta Najeriya, EFCC, ta ce ta bankado wani gwamna na wata jihar arewacin kasar da ya kwashi tsabar kudi har naira biliyan 60 daga asusun jiharsa.

Hukumar ta bayyana haka ne a sakon da take aike wa manema labarai wata-wata mai taken EFCC Alert.

EFCC, wadda ta ambato shugabanta Abdulrasheed Bawa yana yin karin bayani game da batun a hirarsa da mujallar da hukumar take wallafawa, ta ce gwamnan da aka gano na wata jiha ce da ke Arewa ta Tsakiya ko da yake bai fadi sunansa ba.

“Zan iya gaya muku a kyauta cewa sabon sashen da muka bude kan leken asiri yana aiki tukuru.

“Ya bankado abubuwa da dama. Daya daga cikinsu shi ne wani gwamna a wata jiha ta Arewa Ta Tsakiya, inda suka gano cewa cikin shekara shida da suka gabata (mutum daya) ya cire tsabar kudin da suka kai N60 bn.”

“Muna kallon abubuwan da yake yi, kuma ina tabbatar muku cewa bayan mun kammala bincike, za mu sanar da ‘yan Najeriya kan abubuwan da muka yi a bayan fage game da laifukan da ake aikatawa ta amfani da shafukan intanet…,” in ji Bawa.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments