Mahimman batutuwa da dan takarar shugabancin kasa a jam’iyyar PDP ya bayyana a ranar laraba

Bayan shafe tsawon lokaci ana dakon zuwan wannan rana, jam’iyyun siyasa a Najeriya sun fara yawon neman ƙuri’un masu zaɓe a hukumance.

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ba ta yi ƙasa a gwiwa ba, inda ta ƙaddamar da tawagar kamfe ɗinta na takarar shugaban ƙasa a ɗakin taro na International Conference Centre da ke Abuja ranar Laraba.

Ɗan takarar shugabancin kasar Atiku Abubakar da mataimakin sa, Ifeanyi Okowa, da sauran jiga-jigai na cikin waɗanda suka yi jawabai a wurin taron.

“yawancin mutanen da suka taru a nan ƙwararrun ‘yan siyasa ne irina waɗanda siyasa ke gudana a cikin jininsu saboda ƙaunar da suke yi wa mutane da kuma ƙasarsu,” a cewar Atiku.

Duk da cewa babban abin da ya tara su shi ne ƙaddamar da tawagar kamfe, an kuma ƙaddamar da wani littafi da aka rubuta game da hukunce-hukuncen da kotuna suka bayar game da ƙararrakin da Atiku ya shigar a tsawon shekaru mai suna ‘Landmark Constitutional Law Cases in Nigeria; The Atiku Abubakar Cases’.

Sai dai ba a ga Gwamnan Rivers Nyesom Wike ba a wurin taron sakamakon rikicin da ke ci gaba ɗaukar sabon salo tsakaninsa da ɓangaren Atiku. Kazalika, tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan bai halarci taron ba.

Sauran waɗanda suka yi jawabai sun hadar da shugaban tawagar kamfe na Atiku, Gwamna Aminu Tambuwal na Sokoto, da muƙaddashin shugaban PDP, Iliya Damagum, da Sanata Dino Melaye.

An ƙaddamar da littafi kan rayuwar Atiku yayin taron

Ga abu biyar da Atiku ya faɗa yayin jawabin nasa.

‘Taron yau ba na gama-gari ba ne’
Ɗan takarar shugaban ƙasar ya fara jawabinsa da godiya ga jagororin kamfe ɗin, yana mai bayyana su da “masu kishin ƙasa da son al’ummarsu”.

Atiku ya ce muhimmancin taron ne ya sa ba zai wuce shi ba “saboda taron na yau ba gama-gari ba ne”.

A cewarsa: “Yau ba rana ce kamar sauran ranaku. Ƙaddamar da tawagar kamfe ta shugaban ƙasa ba taron gama-gari ba ne. Samsam ba haka ba ne.”

Me zai faru idan ba a warware rikicin APC da PDP nan kusa ba?
22 Satumba 2022
Ba za mu iya aiwatar da buƙatun Nyesom Wike ba – Jam’iyyar PDP
11 Satumba 2022
Ba zan sauka daga shugabancin PDP ba – Iyorchia Ayu
31 Agusta 2022
‘Najeriya ta ɓalɓalce a ƙarƙashin mulkin APC’
Kamar yadda aka saba, duk lokacin da jam’iyyun adawa suka samu dama kan soki APC mai mulki, kamar yadda ita ma take kan soki mai adawa da ita.

A wannan karon, Atiku ya yi iƙirarin cewa Najeriya ta shiga “halin rashin tsari” a ƙarƙashin mulkin APC na shekara bakwai bisa jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari, wadda ta hau mulki a 2015.

“Ƙasarmu ta afka cikin rashin doka da oda. Wannan gwamnatin ta gaza wajen aiwatar da ƙashin bayan abin da aka zaɓe ta a kai; kare rayuka da dukiyoyi,” a cewarsa.

“Kowa ya san haka. Tattalin arzikinmu ya wargaje. Mutanenmu na fuskatar matsin rayuwa a kullum.

“Rashin haɗin kan da muke fama da shi a yanzu ya zarce na lokacin yaƙin basasa. An wargaza zumuncin da ya haɗe kanmu ta hanyar nuna wariya da rashin amincewa da juna.”

‘Tsarin gwamnati yanzu ba na adalci ba ne’
Da yake ci gaba da kokawa kan matsalolin da ya zargi gwamnatin APC da jefa ƙasa, Atiku ya ce tsarin gwamnati a yanzu ya zama “mara adalci”

“Tsarin gwamnati a yanzu cike yake da rashin adalci ta hanyar fifita gwamnatin tarayya da kuma zalintar sauran gwamnatoci, abin da ya zama wata hanya ta jawo rashin ci gaba da kuma cin hanci.

“Irin wannan tsarin bai dace da ƙarni na 21 ba, wanda ake buƙatar ya kusanto da haɓakar tattalin arziki kusa da al’ummarmu.”

‘Muna da tsarin gyara Najeriya’
Bayan lissafo abubuwan da ya bayyana a matsayin matsala, Atiku ya ce jam’iyyarsu ta PDP na da tsarin ceto Najeriya daga ƙangin da take ciki.

“Shirinmu game da Najeriya shi ne ceto ta ta hanyar adalci da daidaito da haɗin gwiwa tsakanin al’ummominmu mabambanta.

“Na biyu shi ne kafa gwamnatin dimokuraɗiyya wadda za ta saka karewa da kuma inganta rayuwar mutane a gaba.

“Na uku, gina tattalin arziki mai ƙarfi da zai samar da dama ga mutane da ƙasa baki ɗaya, sannan ya fitar da miliyoyi daga ƙangin talauci.

“Za mu kafa cikakkiyar gwamnatin tarayya da za ta bai wa kowane mataki na gwamnati dama da wakilci da za su ba da damar kare iyakokinmu da tsaron ƙasa da kuma haɗin kai.”

‘Mun taru ne don ceto Najeriya’
Har yanzu dai game da taron, Atiku ya bayyana cewa ba su taru kawai don ƙaddamar da tawagar kamfe ba, sun taru ne don ceto Najeriya.

“Mene ne abin da ya tara mu a nan? Mene ne aikinmu? Ba mu taru a nan kawai don mu ƙaddamar da tawagar kamfe ba. A’a, ya wuce haka.

“Aikinmu shi ne haɗa kai don ceto ƙasarmu mai albarka. Wannan shi ne babban muradinmu.

“Amma abin da za mu fara yi shi ne ƙwace mulki daga hannun jam’iyyar da ta jefa mu cikin wannan matsalar. Don aiwatar da hakan, dole ne mu haɗa kai mu cinye zaɓukan da ake shirin gudanarwa a shekara mai zuwa.”

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments