Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero,ya bukaci sabon kwamishina yan sandan jihar Kano cp Abubakar Lawan Daura da ya tsaya tsayin daka wajan kare lafiya da dukiyoyin al’umma duba da yanda ake dama da matsalar tsaro a kasar nan.
Sarkin ya bayyana hakan ne lokacin da yake karbar bakuncin sabon kwamishinan yan sandan na jihar Kano cp Abubakar Lawan Daura yayin da ya ziyarce shi a fadar sa.
Alhaji Aminu Ado Bayero,ya ce jihar Kano jihace mai al’umma da dama sai sabon kwamishinan yan sandan da ma’aikatan sa sun kara himma wajan kula da rayuka da dukiyoyin al’umma.
Anasa jawabin sabon kwamishinan yan sandan na jihar Kano cp Abubakar Lawan Daura ya ce, rundunar yan sandan jihar Kano zata cigaba da kokarin ganin ta kula da harkokin tsoran jihar.
shugabanin kungiyoyin masu sana’ar sayar da magungunan gargajiya sun ziyarci fadar Sarkin domin cigaba da bikin ranar masu sana’ar sayar da maganin gargajiya ta duniya.