A karo na biyu ƙasa da mako guda, Hukumar kula da Zirga-zirga Ababen Hawa ta jiha KAROTA ta ƙara cafke mota ƙirar Tirela maƙare da Gina a kan titin Bello Dandago da misalin karfe 2:30 na dare inda , suke ƙoƙarin su na shiga cikin Sabon Garin Kano
Jami’in hulda da jama’a na Hukumar KAROTA Nabulusi Abubakar Kofar Na’isa shi ya tabbatar da hakan ga manema labarai.
K/Naisa yace jamian su sun sami nasarar cafke motar ne a lokacin da suka buƙaci direban motar ya gabatar musu da takardar shaidar abinda ya ɗakko ta Way bill, inda ya bayyana musu cewa Kwali ya ɗakko
Bayan da jami’an suka matsa bincike sai suka tabbatar da Giya ce a cikin babbar motar
Shugaban Hukumar KAROTA Hon Baffa Babba Ɗan’agundi ya bayyana cewa Hukumar KAROTA ba za ta gajiya ba wajen kama duk wani nau’in kayan da aka ci karo da su wanda dokar jihar Kano bata amince a shigo da su ba
Ya ƙara da cewa za a ƙara baza jami’an KAROTA musamman kan manyan titinan jihar nan domin ganin an daƙile shigowar kayayyakin da dokar jihar Kano ta haramta
Ƙasa da mako guda Hukumar ta cafke manyan motocin Tirela maƙare da Giya wadanda adadinta ya kai fiye da Kwalba dubu arba’in (K40)da kuɗinta ya haura naira miliyan arba’in (N40m)
Da zarar an kammala bincike za a miƙa Giyar ga Hukumar Hizba domin ɗaukar mataki na gaba.