Mai martaba sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana irin gudumawar da likitoci suke bayarwa wajen cetan rayukan al’umma da cewa aikine na sadaukar da rayuwa.
Sarkin ya bayyana haka ne lokacin da yake karbar bakuncin shugabanin kungiyoyin likitoci kwararru mata dana kungiyar likitoci masu lura da cutar koda ta kasa yayin da suka ziyarce shi a fadar sa.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya ce aikin da likitoci suke aikine da yake ceton rayuwar al’umma ne duba da yanayin da likitocin suke karbar mara lafiya a lokutan da aka kaishi asibiti.
Ya kuma ce su cigaba da godewa Allah bisa ni’imar da yayi musu wajen samun ilimin cetan rayuwar al’ummar kasar nan.
Da yake jawabin Shugaban sashin kula da masu fama da ciwon koda na asibitin koyarwa na malam Aminu Kano farfesa Aliyu Abdu ya ce, sun ziyarci fadar sarkin ne domin neman albarka duba da taron da zasu gudanar na shekara shekara anan jihar Kano.
Daga AbubakarBalarabe Kofar Naisa Sakataren Yada Labarai na Masarautar Kano